Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, ya nesanta kansa daga rahotannin da ke danganta shi da sabuwar hadakar ‘yan adawa karkashin jam’iyyar ADC, yana mai jaddada cewa har yanzu yana cikin jam’iyyar APC a matsayin mamba na gaskiya kuma mai biyayya ga tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari.
Sirika ya yi wannan karin bayani ne a shafinsa na X, bayan wasu maganganu daga ministan Abuja, Nyesom Wike, da mai ba shugaban kasa Bola Tinubu shawara kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, suka ce ya shiga cikin hadakar adawar.
Hadi Sirika wanda rahoton Jaridar Daily Trust ya bayyana a matsayin daya daga cikin wadanda suka kafa jam’iyyar APC, ya kuma rada mata suna, yace bai da niyyar ficewa daga jam’iyyar.
Inda ya kuma soki Wike da Onanuga, yana mai cewa ya kamata su tabbatar da sahihancin bayanai kafin fitar da su fili.



