Hukumar zaben Nijeriya INEC ta bayyana cewa ta karɓi ƙarin buƙatun rajista guda 12 daga ƙungiyoyin da ke neman zama jam’iyyun siyasa a kasar, inda hakan ya kai yawan waɗanda ke neman rajistar zuwa 122.
INEC ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ƙasa mai kula da Yada Labarai da Ilimin Zaɓe, Mista Sam Olumekun, ya fitar a ranar Alhamis.
Sanarwar ta jaddada cewa ana aiwatar da tantance waɗannan buƙatu cikin gaskiya da adalci, kuma hukumar za ta rika sanar da ‘yan ƙasa ci gaban da ake samu.
Jaridar The Nation ta ce hukumar ta kuma ja hankalin ƙungiyoyin da ke neman rajista da su kasance da daidaito wajen bayyana shugabanninsu don guje wa tsaiko a cikin aikin tantancewa.



