Magoya bayan Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, da na Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, sun yi arangama a ranar Lahadi a harabar fadar Kofar Kudu, yayin da Aminu Bayero ke dawowa daga gidan sa da ke Mandawari.
Rahotanni sun bayyana cewa a yayin arangamar, an fasa kofar fadar, tare da farma masu gadin fada har wasu suka ji rauni, sannan an lalata motoci na ‘yan sanda da ke cikin harabar fadar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
A cikin wata sanarwa da sashen yada labarai na Masarautar Kano ya fitar, wadda Sadam Yakasai ya rattaba wa hannu, ta zargi magoya bayan Aminu Ado Bayero da haddasa rikici a lokacin da Sarki Muhammadu Sanusi II bai nan.
Kokarin samun martani daga bangaren Sarki Aminu Ado Bayero ya ci tura, domin mai magana da yawunsa, Abubakar Kofar-Naisa, bai dauki kiran waya da jaridar ta yi masa ba.
Sai dai Muktar Dahiru, daya daga cikin masu rakiya tare da Bayero kuma wanda ya shaida faruwar lamarin, ya karyata zargin da Sadam Yakasai ya yi.

Magoya bayan Sarki Aminu Bayero da na Sarki Muhammadu Sanusi sun yi rikici a fadar Kofar Kudu
-