DCL Hausa Radio
Kaitsaye

An yanke wa ɗan Najeriya hukuncin ɗaurin shekaru 11 a Amurka kan damfara da ta kai dala miliyan 1.3

-

Wata kotu a Amurka ta yanke wa wani ɗan Najeriya mai zama a San Gabriel Valley, Abiola Femi Quadri, hukuncin ɗaurin shekara 11 da wata 3 a gidan yari, bisa damfarar tallafin COVID-19 da ake bai wa marasa aikin yi da masu lalura ta musamman da ya kai dala miliyan 1.3 daga jihohin California da Nevada.

Quadri, mai shekaru 43, an kama shi ne bayan ya shigar da fiye da buƙatun 100 na bogi ta hanyar amfani da sunayen mutane daban-daban da ya saci bayanansu, kuma ya yi amfani da kuɗin wajen gina wurin shakatawa da kasuwanci a Nijeriya.

Google search engine

Alkalin kotun tarayya ta Amurka, George H. Wu, ne ya yanke hukuncin, tare da umartar Quadri da ya biya kuɗin diyyar dala $1,356,229 da tara na dala $35,000, bayan ya amsa laifinsa.

Sanarwar hakan na kunshe ne cikin wata takardar manema labarai daga ofishin mai gabatar da ƙara na gwamnatin tarayya a gundumar California ta tsakiya, Ciaran McEvoy, a ranar Alhamis, 10 ga Yuli, 2025.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttp://dclhausa.com
Ukashatu Wakili shi ne Mataimakin Editan Gudanarwa kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki na DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Ina nan daram a NNPP, babu inda zan je – Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso

Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa ba shi da...

Takara ta da Makinde za ta yi armashi idan PDP ta amince – Bala Muhammad

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana cewa takarar shi da takwaransa na jihar Oyo, Seyi Makinde, za ta yi armashi idan jam’iyyar PDP ta...

Mafi Shahara