APC mai mulki a Nijeriya da gungun jam’iyyun adawa da suka haɗu ƙarƙashin inuwar jam’iyyar ADC, waɗanda ke shirin kifar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, na ƙoƙarin lashe ƙuri’u miliyan 5.7 na jihar Kano, kamar yadda binciken jaridar PUNCH ya gano. Hakan na zuwa ne yayin da siyasar Nijeriya ke ƙara zafi gabanin zaɓen 2027.
A siyasar Kano dai, akwai tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ke da mabiya da dama ƙarƙashin mazhabar Kwankwasiyya Movement.
Wasu manyan ’yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban da suka tattauna da jaridar sun bayyana cewa ƙuri’un Kano da matsayin Kwankwaso za su taka muhimmiyar rawa wajen tantance sakamakon zaɓen 2027.
Kwankwaso ya tsaya takarar shugabancin Nijeriya a zaɓen 2023 ƙarƙashin jam’iyyar NNPP, inda ya zo na huɗu da ƙuri’u kusan 1.5m, mafi yawan su daga jihar Kano, inda nan ne daben siyasarsa ya fi jin makuba.
A jihar Kano kaɗai, Kwankwaso ya samu ƙuri’u kusan milyan daya a yayin zaben na 2023, wanda ya ba shi damar doke jam’iyyar APC da ke rike da mulki a jihar a wancan lokacin.
Yayin da jam’iyyun adawa irin su PDP da Labour Party ke fama da rikice-rikice na cikin gida, APC da Shugaba Tinubu na cewa ko gezau gabanin 2027. Sai dai fitowar gungun jam’iyyun adawa karkashin ADC a kwanan nan na iya sauya lissafin siyasar gaba ɗaya.
ADC, ƙarƙashin jagorancin tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Atiku Abubakar, tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai, ɗan takarar shugaban ƙasa na LP a 2023 Peter Obi, da ya samu ƙuri’u miliyan 6.1, tsohon gwamnan jihar Osun Rauf Aregbesola, tsohon shugaban majalisar dattawa David Mark, da kuma tsohon gwamnan Rivers Rotimi Amaechi, na ƙara samun karɓuwa tare da janyo wasu manyan ’yan siyasa daga sassa daban-daban na ƙasar.
Yayin da iskar zaben 2027 ke cigaba da kadawa a hankali, Rabiu Musa Kwankwaso na nan a matsayin mutum mai matuƙar muhimmanci, kuma shawararsa ta karshe kan inda zai mara wa baya, na iya rinjayar sakamakon zaɓe musamman a arewacin ƙasar da ke da matuƙar tasiri, in ji binciken jaridar Punch da ta wallafa a shafinta na yanar gizo.
Wasu jiga-jigan siyasa daga APC da gungun ADC sun tabbatar wa da jaridar cewa ana ci gaba da kokarin shawo kan Kwankwaso domin su samu ƙuri’un jihar Kano.
Haka kuma wasu majiyoyi daga NNPP da suka nemi a sakaya sunansu saboda ba su da izinin magana da manema labarai, sun tabbatar cewa shugabannin APC da ADC sun gana da Kwankwaso da wasu fitattun shugabannin NNPP domin tattaunawa kan yiwuwar marawa ko rashin marawa Tinubu baya a zaɓen 2027.
Zuwa yanzu dai Kwankwaso, dai bai cE uffan ba kan inda ya dosa, lamarin da ke ƙara tsananta ruɗanin siyasa ga masu neman tagomashin siyasarsa a ƙasar.