Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun
Allah Ya yi wa tsohon shugaban Nijeriya Muhammad Buhari rasuwa a wani asibiti da ke birnin London. Mai magana da yawunsa Malam Garba Shehu be ya sanar da hakan da yammacin Lahadin nan. Ya rasu yana da shekaru 83.
Rasuwar tasa ta zo ne bayan makonnin da aka kwashe ana jinyarsa a London, inda tsohon mai magana da yawun Buharin ya sanar a kwanakin baya cewa Buharin ya fara samun sauki.
Tuni shugaba Tinubu mai ci ya fitar da sanarwar inda ya nuna damuwa kan wannan rashi. Ya ce ya yi magana da Aisha Buhari, inda ya nuna alhininsa ya kuma umurci mataimakinsa Kashim Shettima ya tafi London don dawo da gawar Buharin zuwa Nijeriya. Kazalika Shugaba Tinubu ya umurci a yi gaggawar saukar da tutocin Najeriya kasa domin jimamin mutuwar tsohon aminin nasa a siyasance.
An dai haifi Muhammadu Buhari a ranar 17 ga watan Disamba, shekara ta 1942, a garin Daura na jihar Katsina. Ya tashi ne a cikin unguwar Daura tare da mahaifiyarsa bayan rasuwar mahaifinsa tun yana É—an shekara hudu.
Ya shiga rundunar sojan Najeriya a shekarar 1961, inda ya yi horo a Najeriya da kuma kasashen waje, ciki har da Ingila da Amurka. Buhari ya taka rawar gani a yakin basasa na Najeriya, sannan daga baya aka naÉ—a shi Gwamnan Soja na jihar Arewa maso Gabas a shekarar 1975. Haka kuma, ya rike mukamin Ministan Albarkatun Man Fetur daga 1976 zuwa 1978, a karkashin mulkin soja na Olusegun Obasanjo.
A ranar 31 ga Disamba, shekarar 1983, Buhari ya jagoranci juyin mulki da ya kifar da gwamnatin Shehu Shagari. Nan take ya zama shugaban Ć™asa na soja. A lokacin mulkinsa, ya kafa shirin War Against Indiscipline wato Yaki da Rashin Da’a, da nufin farfado da É—abi’un jama’a da yaki da cin hanci. Sai dai an siffanta mulkinsa da mai tsanani da tauye ‘yancin jama’a.
Amma a ranar 27 ga watan Agusta, shekarar 1985, wani juyin mulki karkashin Ibrahim Babangida ya kifar da gwamnatin Buhari, inda aka tsare shi har zuwa 1988.
Bayan shekaru, Buhari ya koma siyasa. Ya tsaya takara a 2003, 2007 da 2011 amma bai yi nasara ba. Sai a 2015, lokacin da ya tsaya takara karkashin jam’iyyar APC, ya samu nasara a kan shugaba Goodluck Jonathan – wanda hakan ya zama karo na farko da shugaba mai ci ya sha kaye a zabe a tarihin Najeriya.
A shekarar 2019, an sake zabensa a wa’adi na biyu. Mulkinsa ya mayar da hankali kan yaki da cin hanci, karfafa tsaro, da kokarin farfado da tattalin arziki. Amma ya fuskanci suka da ƙalubale da dama ciki har da hauhawar farashi, rashin tsaro, da dogon hutun jinya a kasashen waje.
A ranar 29 ga Mayu, shekarar 2023, Buhari ya mika mulki ga Bola Ahmed Tinubu bayan kammala wa’adin mulki na shekara takwas.