Manhajar TikTok ta goge fiye da bidiyo miliyan 3.6 a Najeriya saboda saba ka’idar dokokinta
Shafin sada zumunta na Tiktok ya cire bidiyo sama da miliya 3 da dubu dari 6 a Nijeriya tsakanin watan Janairu zuwa Maris na 2025 sakamakon saba dokokin amfani da shafin nasu.
Wannan adadin wanda yake wakiltar karin kaso 50 na wanda aka cire a baya.
Manhajar ta TikTok ta sanar da hakan ne a wani rahoto na farkon shekara game da dokokin amfani da shafin wanda ke nuna kokarin kamfanin TikTok din wajen kare masu amfani da shafin, mutuntawa da kuma yarda.
Kamfanin ya kara da cewa, wadanda aka cire na wakiltar kaso karami idan aka kwatanta da sauran da ke da ilimantarwa, nishadantarwa da kuma amfani.