Wani dutsen sararin samaniya da aka gano a yankin Agadez na Jamhuriyar Nijar a watan Nuwamba 2023 ya zama babban ɓangaren dutse daga duniyar Mars da aka taɓa gani a duniya.
An sayar da shi a ranar Laraba a cibiyar kasuwancin Sotheby’s da ke birnin New York kan kudi dala miliyan 4.3 kimanin fam miliyan 3.2, kamar yadda kafar BBC ta ruwaito.
Dutsen, wanda aka fi sani da NWA 16788, yana da nauyin kilogiram 24.5, kuma tsawonsa ya kai sentimita 38.1 (inchi 15).
Masana sun ce dutsen ya fi girma da kashi 70% fiye da duk wani dutsen Mars da aka taɓa ganowa a doron duniya.
An gano wannan dutse mai daraja a cikin hamadar Nijar ne, inda ba kasafai ake samun motsin jama’a ba.



