Fitaccen dan siyasa, jigo a jamiyyar hadaka ta ADC a Jihar Katsina, kuma tsohon sakataren gwamnatin jihar ya fadi hakan ne a wata tattaunawar sa da DCL Hausa kwanaki kadan bayan sun kaddamar da jam’iyyar ADC a jihar
Jam’iyyun APC, PDP da NNPP a jihar sun gamu da babban koma baya, bayan dubban jiga-jigan ‘ya’yan jam’iyyun suka sauya sheka zuwa sabuwar hadakar ta ADC.
Daga cikin jiga-jigan PDP da suka koma ADC akwai tsohon sakataren gwamnatin jihar, Dr Mustapha Muhammad Inuwa da tsohon ministan tsaro a Nijeriya Lawal Batagarawa da tsohon sanata a shiyyar Daura Ahmed Babba Kaita da kuma Janar Maharazu Tsiga mai ritaya da sauran su.
Tsohon sakataren ya ce sabon taken jam’iyyar ADC a Katsina “Nijeriya kowa yana ji a jikin shi, Katsina kuma akwai korafi.