Gwamnatin Faransa ta kammala janye dakarunta daga ƙasar Senegal bayan shekaru 65 da girka sansanonin soja a ƙasar tun bayan samun ‘yancin kai.
A wani taron miƙa ikon da aka gudanar a Dakar, jami’an gwamnati daga Faransa da Senegal sun halarci bikin miƙa sansanin Camp Geille — mafi girma daga cikin sansanonin Faransa a ƙasar — da kuma filin tashi da saukar jiragen sama da Faransa ke amfani da shi a filin jirgin Dakar.
Matakin na zuwa ne a matsayin wani bangare na janyewar Faransa daga tsofaffin ƙasashen da ta yi wa mulkin mallakanta a Afirka, inda ƙasashe ke ƙara buƙatar ‘yanci da ikon gudanar da harkokin tsaro ba tare da tsoma bakin ƙasashen Turai ba.


