DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Mun cika kashi 85 cikin 100 na alkawuranmu ga al’ummar Kano – Gwamna Abba Gida Gida

-

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta riga ta aiwatar da kashi 85 cikin 100 na alkawuran da ta dauka lokacin yakin neman zabe, yana mai cewa saura kashi 15% kacal kafin a cika kafin ya kammala mulki.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yau Alhamis yayin rantsar da sabon shugaban ma’aikata na fadarsa, Dr Sulaiman Wali Sani, tare da shugaban hukumar ayyuka na  usamman, Manjo Janar Sani Muhammad (rtd), da kuma nasu ba da shawara na musamman guda 11.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Gwamna Abba na cewa, wannan ci gaba ya samo asali ne bayan ingantaccen nazari da kimantawa da  gwamnatinsa ta gudanar cikin shekaru biyu da suka gabata.

Gwamnan ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa ba za ta tsaya nan ba, domin akwai shirin kawo sabbin tsare-tsare da shirye-shirye domin ƙara inganta rayuwar al’ummar jihar.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttp://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Babban Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Za mu fara hukunta duk wani dan kasar waje da wa’adin bizarsa ya kare a Nijeriya kuma ya ci gaba da zama – Gwamnatin...

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa yanzu tana da cikakken tsarin gano tare da cafke baƙin ƙasashen waje da suka wuce wa’adin zaman da aka ba...

Obasanjo ya nuna jarumtaka da sadaukarwa wajen yi wa Nijeriya hidima – Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo murnar cika shekaru 89 da haihuwa. A cikin wata sanarwa da mai magana da...

Mafi Shahara