Kungiyar Kwadago ta Nijeriya (NLC) ta bayyana rashin jin daɗinta kan yadda ƙasar ta ƙara faɗawa cikin jerin ƙasashen da ke da mummunan tarihin take haƙƙin ma’aikata a duniya.
Shugaban NLC, Comrade Joe Ajaero, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Adewale Adeyanju, ya bayyana haka ne a lokacin taron shekara-shekara karo na 68 na ƙungiyar NECA (Nigeria Employers’ Consultative Association) da aka gudanar a birnin Lagos a ranar Laraba.
A cewarsa, sabon rahoton na ITUC Global Rights Index na 2025 ya sanya Najeriya cikin ƙasashe 10 a duniya da suka fi take haƙƙin ma’aikata.
Ajaero ya ƙara da cewa da yawa daga cikin take haƙƙin ma’aikata da rahoton ya ambata, na faruwa ne a cikin manyan kamfanoni da cibiyoyin kasuwanci da ke cikin ƙungiyar NECA.
Najeriya na cikin ƙasashe 10 a duniya da suka fi take haƙƙin ma’aikata – Binciken ICTU Global Index
-


