Hedkwatar tsaron Nijeriya ta bayyana cewa ƙasar na da cikakken ‘yanci da ikon yanke shawara da kanta, musamman a batutuwan tsaro da yaki da ta’addanci.
Wannan martanin na zuwa ne bayan wasu kalaman da Jakadan Turkiyya a Najeriya, Mehmet Poroy, ya furta a Abuja a ranar Talata, inda ya yi zargin cewa wasu mambobin ƙungiyar da gwamnatin Turkiyya ke kiran Fethullah Terrorist Organisation (FETO) na gudanar da ayyukansu a Nkjeriya karkashin sunan makarantu da cibiyoyin lafiya.
Amma yayin wani taron manema labarai a Abuja a ranar Alhamis, Daraktan huldar da jama’a na hedkwatar Manjo Janar Markus Kangye, ya bayyana cewa wannan zargi ba shi da tushe a hukumance a wajen rundunar.
Ya ƙara da cewa Nijeriya ba za ta saurari kowanne irin bayani daga waje ba, muddin bai da tushe a cikin bayanan leƙen asirin ƙasa da take tattarawa.
Nijeriya ba za ta yarda a yi mata katsalandan kan tsaro ba – Martanin hedkwatar tsaro ga Jakadan Turkiyya
-


