Rundunar ‘Yan sandan Jihar Kano ta tabbatar da cafke ɗalibai 11 na makarantar Government Boarding Secondary School, Bichi, bisa zargin hannu a kisan wasu ɗalibai biyu a cikin makarantar.
Mai magana da yawun rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da hakan a wata saƙo da ya aike wa jaridar Punch a ranar Alhamis.
Ya bayyana cewa an kama ɗaliban ne domin tambayoyi da bincike kan yadda lamarin ya faru da kuma matsayin kowanne daga cikinsu a cikin wannan aika-aika.
Rahotanni sun nuna cewa waɗanda aka kashe, Hamza Idris Tofawa da Umar Yusuf Dungurawa, sun rasu ne sakamakon harin da wasu ɗalibai suka kai musu da wasu ƙarafa da ake kira “Gwale-Gwale”.
A baya, Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Dr. Ali Haruna Makoda, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan kisan ɗaliban.
