Hukumar raya babban birnin tarayya Abuja (FCTA) ta ce an kama mutane 210 da ake zargi da barace-barace da wasu laifuka daban-daban, a wani sabon yunkuri da take kawar da barace-barace daga titunan Abuja.
Daraktar rikon kwarya ta sashen jin ƙai da kula da walwalar jama’a, Gloria Onwuka, ce ta bayyana hakan yayin miƙa waɗanda aka kama zuwa cibiyar gyaran halaye da ke Bwari, a cewar gidan talabijin na NTA.
Gloria ta ce waɗanda aka kama sun haɗa da mata, maza da yara waɗanda ke barace-barace a manyan tituna, da kuma wasu da ake zargi da aikata laifuka daban-daban.
