Shugaban riko na jam’iyyar PDP Ambasada Iliya Damagum, ya bayyana ficewar tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, daga jam’iyyar a matsayin wani lamari da ba sabon abu ba.
Da yake zantawa da manema labarai a Bauchi ranar Juma’a, Damagum ya ce jam’iyyar PDP ba ta ji wani mamaki ko damuwa ba dangane da ficewar Atiku, domin ya saba da irin wannan a shekarun baya.
“Yana cikin tsarin da muka saba da shi — ya tafi, ya dawo. Wannan wani salo ne na siyasarsa, ba mu ɗauke shi a matsayin rabuwa ta dindindin ba,” in ji Damagum.
Wannan na zuwa ne yayin da rahotanni ke cewa Atiku na ƙoƙarin shiga jam’iyyar hadaka ta ADC a hukumance, a shirin tunkarar zaɓe mai zuwa.



