Shugaban Amurka Donald Trump ya kamu da matsalar jini a ƙafafu, amma ba mai hatsari ba, a cewar Fadar White House a ranar Alhamis.
Mai magana da yawun Fadar Shugaban Ƙasa, Karoline Leavitt, ta ce an gano cewa Trump yana da chronic venous insufficiency — wata matsala ta rashin zagayawar jini yadda ya kamata a ƙananan sassan jiki.
Trump mai shekaru 79, ya fara ganin kumburi a ƙafafunsa cikin makonnin da suka gabata.
Game da bakin tabon da aka gani a hannunsa na dama, Fadar White House ta ce hakan ya faru ne saboda yawan gaisawa da mutane da kuma shan maganin aspirin, wanda yake kariya daga matsalolin zuciya.
Fadar White House ta bayyana cewa babu wata matsala mai haɗari da ke tattare da lafiyarsa.