Jigo a jam’iyyar PDP, Cif Bode George, ya bayyana cewa mutanen da suka haifar da rikicin cikin gida a jam’iyyar su ne ke barin jam’iyyar yanzu, yana mai nuni da ficewar tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a 2023, Atiku Abubakar, da Dele Momodu, wanda shima ya fice daga jam’iyyar a ranar Alhamis.
Cif Bode George ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels TV a ranar Alhamis.
Yayin da yake mayar da martani kan ko PDP za ta iya tsayawa da ƙafafunta bayan ficewar fitattun mutane kamar Atiku da Dele Momodu.
Ya kuma bayyana cewa jam’iyyar PDP za ta koma kan turbar da ta dace bayan taron kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) da aka shirya gudanarwa mako mai zuwa.


