Tsohon shugaban ma’aikata na Marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, Farfesa Ibrahim Gambari, ya bayyana yadda wasu makusantan shugaban suka rika tsallake shi tare da mika takardu kai tsaye domin ya sanya musu hannu.
Farfesa Gambari ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Inside Sources na Channels Television a ranar Juma’a.
A cewarsa, duk da cewa Shugaba Buhari ya bayyana cewa dole ne duk wasu takardu su rika bi ta hannun shugaban ma’aikata, wasu daga cikin mukarrabansa suna amfani da saukin zuciyarsa da sanin lokutan rauninsa, suna mika bukatunsu kai tsaye.
Farfesa Gambari, wanda ya rike mukamin daga Mayu 2020 zuwa Mayu 2023 bayan rasuwar Abba Kyari, ya ce ko mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ta hanyarsa yake tura takardunsa amma ‘yan cabal sai dai su tsallake sa.



