Sojoji 559 ne shugaban kasar Togo ya dauki matakin kora daga aikin sojan
A cewar majiyar hukumomin kasar wannan mataki ya biyo bayan kauracewa wajen aiki da wadannan sojoji suka yi na tsawon lokaci ba tare da wata hujja ba
Takardar sunayen sojojin da matakin ya shafa tuni aka mika ta ga babban hafsan tsaron kasar janar Dimini Allahare domin aiwatar da matakin nan take
Wannan mataki a cewar hukumomin Togon na da manufar karfafa da’a da ladabi a cikin rundunar sojin kasar da kuma tsabtace adadin dakarun
Kazalika hukumomin sun ce zai kara tunatar da alkawalin bada kai domin yin aiki da ake dauka musamman a irin wannan lokaci da yankin kasashen ke fama da matsalar tsaro