Sufeto Janar na ‘yan sandan Nijeriya, Kayode Egbetokun, ya bayyana cewa ba shi da ikon cire tsofaffin jami’an ‘yan sanda daga tsarin fansho na Contributory Pension Scheme, yana mai jaddada cewa lamarin yana buƙatar matakin dokoki daga majalisar tarayya da sauran hukumomin gwamnati.
A ranar Litinin, tsofaffin ‘yan sanda daga sassa daban-daban sun gudanar da zanga-zanga a majalisar tarayya da kuma hedikwatar rundunar ‘yan sanda a Abuja, suna ƙorafi kan wahalhalu da rashin adalci da suke fuskanta a tsarin fansho da aka sanya su ciki.
IGP Egbetokun, yayin da ya karɓi tawagar shugabannin masu zanga-zangar, ya bayyana damuwarsa da halin da suke ciki.
Ya kuma tabbatar musu da cewa an fara tattaunawa da hukumomin da suka dace domin duba yiwuwar fitar da jami’an ‘yan sanda daga tsarin CPS zuwa tsarin fansho na gargajiya, tare da tabbatar da walwala da mutuncin dukkan masu ritaya.




Allah ya kawo musu mafita ta alkairi kuma ya shiga tsakanin su da azzalumai