Dakatacciyar Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta cika alkawarinta na komawa bakin aiki a majalisar dattawan Nijeriya, biyo bayan hukuncin kotu da yace a mayar da ita.
Natasha ta bayyana a harabar Majalisar Tarayya da misalin ƙarfe 12:20 na rana ranar Talata tare da gungun mutanen da suka yi mata rakiya, ciki har da fitacciyar mai rajin kare ‘yancin bil’adama, Aisha Yesufu, da wasu masu goyon bayan yunkurinta.
Sai dai, jami’an tsaro sun dakatar da Natasha daga shiga ginin babban zauren Majalisar Dattawa, duk kuwa da cewa ta bayyana a fili cewa zata dawo bakin aiki a wannan Talata.
Rahotanni sun nuna cewa an ƙara tsaurara matakan tsaro a Majalisar tun kafin zuwan Natasha, inda jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda, jami’an Civil Defense, da kuma DSS suka rufe babbar ƙofar shiga majalisar, tare da tsaurara bincike.
Wannan mataki ya janyo dogon layin motoci a ƙofar shiga majalisar, yayin da jami’an tsaro ke ƙoƙarin tabbatar da cewa Natasha ba ta iya ketare shingen bincike ba.
Wasu daga cikin magoya bayan Sanatar da suka rako ta zuwa Majalisar Tarayya an ji suna rera waka da harshen Pidgin suna cewa: “Sanatar mu ce wannan, ba mu da wata sai ita,” inda wasu ke amsawa da: “Eh ita ce Sanatarmu”
Daga bisani dai Natasha, ta sauka akan motoci tare da yin tattaki domin shiga majalisar kamar yadda ta yi alkawari a baya.
Majalisar Dattawa ta riga ta yi mata kashedi da ta dakatar da yunkurin komawa aiki da karfi da yaji kafin kammala wa’adin dakatarwarta.
A gefe guda, Majalisar Dattawa ta sake jaddadawa karo na uku – cewa babu wani hukuncin kotu da ya tilasta mata dawo da Natasha bakin aiki kafin wa’adin dakatarwar ya cika.



