Jam’iyyar APC na iya nada sabon shugaban jam’iyya na kasa a gobe Alhamis, yayin babban taron kwamitin zartaswa na kasa (NEC) da za a gudanar a Abuja.
Rahotanni sun bayyana cewa tsohon shugaban jam’iyyar, Abdullahi Umar Ganduje, ya sauka a watan Yuni bisa dalilin rashin lafiya.
Sai dai majiyoyi daga sakatariyar jam’iyyar sun ce babban abinda za a tattauna a taron NEC din ya hada da zabin sabon shugaba, sake duba kundin tsarin mulki da kuma batun shirya tarukan Congress a matakai daban-daban.
Wata majiya ta ce yawancin shugabannin jam’iyyar na goyon bayan Ali Dalori ya ci gaba da rike kujerar shugabancin jam’iyyar na rikon kwarya.



