Tsohon dantakarar gwamnan Jigawa a jam’iyyar NNPP malam Aminu Ringim, ya bayyana cewa tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, shi ne kaɗai ɗan siyasar da ya cancanci maye gurbin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a Arewacin Najeriya bayan rasuwarsa.
A wata ganawa da manema labarai a Abuja ranar Talata, Malam Aminu Ringim ya ce Kwankwaso ya gina kyakkyawar kafa ta ci gaban dan adam da na ababen more rayuwa lokacin da yake gwamnan Kano, wanda hakan ya nuna cancantarsa wajen rike ragamar jagoranci a yankin Arewa.
Malam Aminu wanda shine ya tsaya wa NNPP takarar gwamnan Jigawa a zaben 2023 yace sanannen al’amari ne jar hula da mabiya Kwankwasiyya ke sawa ba alama ba ce kawai, fassara ce ta gwagwarmaya da jajircewar kawo ci gaba, da kuma cigaban tunanin Aminu Kano da ya dace da karni na 21.



