Mazauna wasu yankuna da dama a karamar hukumar Gusau ta jihar Zamfara sun gudanar da zanga-zangar lumana a ranar Laraba, suna neman daukin gaggawa daga gwamnati don dakile karuwar hare-haren ‘yan bindiga a yankunansu.
Zanga-zangar, wadda ta fara da misalin karfe goma sha biyu na rana, ta hada da gungun jama’a masu yawa, wasu a kan babura, wasu cikin motoci, da kuma wasu na tafiya a kasa, suka ratsa birnin Gusau har suka isa kofar gidan gwamnatin jihar.
Kauyuka da suka hada da Mada, Ruwan Bore, Fegin Baza, Bangi, Lilo, Wonaka, da Fegin Mahe sun fuskanci hare-hare sau da dama, inda mazauna yankunan suka ce sama da mutum 100 ne aka kashe cikin watannin da suka gabata.
Daya daga cikin masu zanga-zangar, Malam Abubakar Abdullahi daga Fegin Mahe, ya bayyana cewa ya rasa ‘yan’uwansa da dama sakamakon rikicin, kuma an kwashe masa kaya da darajarsu ta haura naira miliyan daya daga shagonsa, ciki ha da buhunan taki guda 500.
Haka zalika, rashin tsaro ya dakile harkokin noma, inda mazauna yankunan ke cewa ya zama hadari matuka su fita noma a gonakinsu kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.