Prof. Nentawe Yilwatdadai shi ne ministan jin kai da yakar fatara na Nijeriya daga jihar Plateau.
Idan dai ba wani sauyi aka samu ba, Ministan Harkokin Jin kai da rage fatara, Prof Nentawe Yilwatda, zai bayyana a yau a matsayin sabon shugaban jam’iyyar APC mai mulki na kasa.
Majiyoyi da dama da suka tattauna da jaridar Daily Trust sun nuna cewa Nentawe shi ne ke kan gaba wajen samun wannan mukami. Sai dai wasu majiyoyi sun bayyana cewa tsohon gwamnan Jihar Nasarawa, Sanata Umaru Tanko Al-Makura, ma yana cikin wadanda ake ambata.
Nentawe dan asalin Jihar Filato ne da ke Arewa ta Tsakiyar Nijeriya, yankin da aka ware tun farko don samar da shugaban jam’iyyar na kasa kafin a nada tsohon gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya yi murabus a farkon wannan wata.
Wasu majiyoyin sun shaida wa Daily Trust cewa har yanzu ana daukar Al-Makura a matsayin zabi na biyu idan wani abu ya faru.