An haifi Janar Hassan Usman Katsina a ranar 24 ga Yuli, 1933. Ya halarci makarantar firamare ta Kankiya da makarantar sakandare ta Katsina (Katsina Middle School). Bayan kammala sakandare, ya tafi Barewa College da ke Zariya, sannan ya ci gaba da karatu a Nigerian School of Arts, Sciences and Technology, a Zariya.
Ya shiga aikin soja a shekarar 1956. Shi ne Gwamnan Soja na farko na tsohuwar jihar Arewa. A lokacin yakin basasa na Nijeriya, Hassan Chiroma ya rike mukamin Babban Jami’in Tsare-tsaren Soji (Chief of Staff, Army), daga baya kuma ya zama Mataimakin Babban Jami’in Tsare-tsare na Hedikwatar Mulki (Supreme Headquarters) a karkashin mulkin Janar Yakubu Gowon.
Ya rasu ne a ranar 24 ga watan Juli, 1995.