Jakadan Tarayyar Turai (EU) a Nijeriya da ECOWAS, Gautier Magnot, ya bayyana cewa sama da yara miliyan biyu da ke fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki a yankunan Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma, inda suke bukatar karin abinci da magani domin ceton rayuwarsu.
Magnot ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da Channels Television a shirin The Morning Brief ranar Juma’a, inda ya ce janyewar taimako daga Amurka da wasu abokan hulda ya bar gibi mai girma, a kokarin tallafawa wadannan yara da abincin tamowa da suka dogara da shi.
Ya ce akwai bukatar gaggauta daukar mataki domin cike gibi da kuma kare rayukan yaran da ke cikin hadari matuka sakamakon yunwa da rashin abinci mai gina jiki.

Cutar Tamowa ta galabaitar da yara miliyan biyu a Arewa ta Gabas da maso Yammacin Nijeriya – Jakadan Tarayyar Turai
-