Jam’iyyar SDP ta bayyana cewa tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ba mambanta ba ne, tana zarginsa da keta doka da kokarin nuna kansa a matsayin wakilin jam’iyyar ba tare izini ba.
A wani taron manema labarai da ta gudanar a Kaduna ranar Juma’a, Sakataren SDP na shiyyar Arewa maso Yamma, Alhaji Idris Inuwa, ya bayyana cewa “El-Rufai ba mamban jam’iyyar SDP ba ne kuma bai taɓa zama ba.”
Ya kuma gargadi jama’a da masu ruwa da tsaki da su yi watsi da duk wata magana da yayi da sunan jam’iyyar.
Inuwa ya ce: “Ya zama dole a fayyace – Malam El-Rufai ba shi da wani izini ko wakilci daga SDP a kowane mataki. Abinda yake yi wani babban laifi ne na keta doka da kuma neman bata wa jam’iyyar suna.”