Hukumomin birnin Yamai sun dauki matakin hana zanga zangar lumana da kungiyar farar hula ta MINNJE ta kuduri aniyar yi, domin nuna bukatar a sako tsohon shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum
A cikin wata takarda mai dauke da sa hannun magajin garin birnin Yamai Kanal Boubacar Soumana Garanké, hukumomin sun ce sun hana gudanar da zanga zangar ne saboda dalilai na tsaro
A ranar 21 ga watan nan ne dai kungiyar ta Mouvement Indépendant pour un Niger Nouveau dans la Justice et l’Egalité, ko kuma MINNJE a takaice, ta aike wa magajin garin birnin Yaman takardar bukatar gudanar da zanga-zangar lumanar.

Gwamnatin Nijar ta haramta zanga-zangar neman a saki Bazoum bayan shekaru biyu da juyin mulki
-