Rashin jituwa ya kunno kai a cikin shugabancin majalisar dattawan Najeriya, biyo bayan sabani da ya fito a fili tsakanin Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da Jagoran Majalisar, Opeyemi Bamidele, kan salon jagorancin Akpabio, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.
Rigimar da ta faru a zaman majalisa na ranar Laraba ita ce sabuwar alamar rikici da ke ci gaba da dabaibaye zauren majalisar, musamman tsakanin manyan kusoshin jam’iyyar APC mai mulki.
Ko da yake an sha musanta labaran da ke nuna akwai rikici a cikin shugabancin majalisar, majiyoyi sun bayyana cewa sabanin da ya biyo bayan zaben Akpabio a matsayin shugaban majalisar a 2023 har yanzu yana nan.
Wasu daga cikin manyan ’yan majalisar na bayyana damuwa a sirrance kan yadda suke kallon salon jagorancin Akpabio a matsayin mai danniya da fifita kansa.

Jagororin majalisar dattawa Akpabio da Bamidele sun samu rashin jituwa kan salon jagoranci
-