Hukumar kula da lantarki ta Nijeriya (NERC) ta bayyana cewa gwamnatocin jihohi ba su da ikon mallakar rumbun wutar lantarki ta kasa (national grid) ko kuma tashoshin wutar lantarki da aka kafa bisa dokokin tarayya ko wadanda ke aiki da lasisin da hukumar ta bayar.
Hukumar ta fadi hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar domin mayar da martani kan cece-kuce da ya biyo bayan matakin Hukumar Lantarki ta Jihar Enugu da ta rage kudin wutar Band A.
A cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, hukumar NERC ta bukaci gwamnatocin jihohi da su sanya farashin wutar da ya yi daidai da kudin sayen wutar gaba daya ko kuma su shirya su biyan tallafi idan suka rage farashin fiye da yadda ya kamata.
