Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan rawar da ake zargin Kwamishinan Sufuri na jihar, Alhaji Ibrahim Namadi, ya taka a sakin wanda ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi, Sulaiman Aminu Dan Wawu.
Gwamnan ya dauki wannan mataki ne bayan samun ƙorafe-ƙorafe daga al’umma, biyo bayan bayyana sunan kwamishinan a wasu takardu na kotu da aka yi amfani da su wajen sakin wanda ake zargin.
Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Asabar.
Sanarwar ta ce Gwamna Abba ya kafa kwamitin bincike na musamman ƙarƙashin jagorancin Barista Aminu Hussain, mai ba shi shawara kan harkokin shari’a da kundin tsarin mulki don tabbatar da gaskiya da adalci.

Gwamnan Kano ya ba da umurnin binciken kwamishinansa da ake zargin ya yi belin dilan miyagun kwayoyi
-