Jam’iyyar PDP na ci gaba da tattaunawa da Peter Obi, tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa a 2019, domin duba yiwuwar dawowarsa cikin jam’iyyar gabanin zaben 2027.
Tsohon ministan ya labarai kuma daya daga cikin ‘yan PDP na farko, Farfesa Jerry Gana ne ya tabbatar da hakan, yayin wani shiri a gidan talabijin na AIT ranar Juma’a, inda ya ce yana jagorantar tawagar da ke tuntubar tsofaffin ‘yan jam’iyya da fitattun ‘yan siyasa daga Kudu.
Rahoton Jaridar Premium Times ya ruwaito cewa Obi ya fice daga PDP a Mayu 2022, kwanaki kafin zaben fidda gwani, yana mai cewa yanayin jam’iyyar ba zai ba da dama ga gina kasa.
Sai dai tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose, ya bayyana rashin kwarin gwiwa a jam’iyyar, yana mai cewa PDP na fuskantar barazana a zaben 2027.



