By Salisu Ado Sulaiman
Tsohon shugaban hukumar kula da wutar lantarki na Najeriya Sam Amadi, yace tulin bashi na iya zama sanadiyyar da gwamnatin tarayya za ta janye tallafin da take zubawa a bangaren.
Amadi ya bayyana haka ne a tattaunawar sa da gidan talabijin na Channels, sai dai ya ce muddin gwamnatin tayi haka ba dabara bace, duba da yadda kasashen da suka ci-gaba ke samar da wutar lantarki a farashi mai rahusa.
Kan matsalar ta wutar lantarki da Najeriya ke fama da ita, tsohon shugaban hukumar ya nuna damuwa da irin rawar da rashin kayan aiki masu inganci da kuma cin hanci da rashawa ke takawa.



