DCL Hausa Radio
Kaitsaye

SDP ta kori El-Rufa’i, ta haramta masa alaka da jam’iyyar na tsawon shekaru 30

-

Kwamitin gudanarwa na kasa NWC na jam’iyyar SDP ya kori tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, daga jam’iyyar na tsawon shekaru 30, bisa zargin karya doka da rashin bin tsarin jam’iyya.

A cewar sanarwar da mai magana da yawun jam’iyyar, Araba Rufus Aiyenigba, ya fitar, El-Rufai bai yi rijista da SDP a matakin mazaba ba, duk da cewa ya bayyana kansa a kafafen sada zumunta a matsayin mamba cikin jam’iyyar.

Google search engine

Jam’iyyar ta kara da cewa El-Rufai ya kitsa labaran karya, ya hada daftarin bogi na membobinsa, ya dauki hoto da shugabannin jam’iyya da aka dakatar domin nuna alamar cewa yana da cikakken iko, da nufin ya dagula tsarin cikin gida da hada jam’iyyar da wata hadakar siyasa ba tare da izini ba.

Jam’iyyar ta ce hukuncin da ta dauka na korar El-Rufai ya samo asali ne daga bincike mai zurfi da ta gudanar kan ikirarin da ya yi na zama dan jam’iyyar da kuma ayyukan sa na gefe da suka saba da tsarin dokar jam’iyyar kamar yadda rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Za mu fara hukunta duk wani dan kasar waje da wa’adin bizarsa ya kare a Nijeriya kuma ya ci gaba da zama – Gwamnatin...

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa yanzu tana da cikakken tsarin gano tare da cafke baƙin ƙasashen waje da suka wuce wa’adin zaman da aka ba...

Obasanjo ya nuna jarumtaka da sadaukarwa wajen yi wa Nijeriya hidima – Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo murnar cika shekaru 89 da haihuwa. A cikin wata sanarwa da mai magana da...

Mafi Shahara