Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana cewa duk da rasuwar tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, shugaba Bola Tinubu zai samu goyon bayan jama’ar Arewa a zaben 2027 mai zuwa.
Rahoton jaridar Punch, ya ambato Sanatan na cewa yadda Buhari ya gina masoya masu tsananin biyayya, haka ya kuma fuskanci tsananin suka daga wasu, musamman matasan Gen Z.
Shehu Sani ya ce Buhari ya kafa irin farin jini da kowa ke muradi, amma hakan yana zuwa da nauyi da kuma bukatar cika alkawura dari bisa dari.
Ya kuma jaddada cewa Tinubu zai iya ci gaba da samun goyon bayan Arewa saboda ya fahimci dabarar siyasar yankin.



