Wasu ƴan bindiga sun yi ajalin mutane 38 daga ƙauyen Banga, karamar hukumar Kauran-Namoda ta jihar Zamfara, duk da cewa an biya su kuɗin fansa fiye da Naira 50 miliyan.
Shugaban karamar hukumar Kauran -Namoda, Mannir Haidara Kaura, ya tabbatar da cewa 56 ne aka sace, amma 18 daga ciki ne kacal suka dawo a raye bayan biyan fansar.
Ya ce an kwantar da waɗanda suka dawo a asibiti domin samun kulawar likitoci, kana gwamnatin jihar tana shirin ziyartar iyalan waɗanda suka rasu sakamakon waki’ar.
Rahoton gidan talabijin na Channels ya ce wani mazaunin ƙauyen, Ibrahim Banga, ya bayyana cewa ƴan bindigar sun nemi Naira miliyan 1 a kan kowanne mutum, amma bayan biyan kuɗin, sai suka kashe sauran 38 cikin zalunci.



