Wani manomi mai shekaru 49 mai suna Musa Yahaya Kala ya rasa ransa bayan da giwaye suka kai masa hari a kauyen Itasin da ke karamar hukumar Ijebu East, Jihar Ogun.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da hantsi a ranar Litinin, inda manomin ke tare da dansa lokacin da giwayen suka kai harin.
Rahoton Jaridar Daily Trust ya ce al’ummar yankin sun bayyana fargaba da fusata kan yadda ake ta fuskantar rikici tsakanin mutane da dabbobin jeji a yankin sau da dama.



