Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume, ya bayyana cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na shirin farfado da tsohon kamfanin masana’antar Kaduna Textile domin ƙarfafa tattalin arzikin ƙasa.
Akume ya bayyana haka ne a taron kwanaki biyu na tattaunawa tsakanin gwamnati da ‘yan ƙasa da aka shirya a Kaduna, karkashin jagorancin cibiyar Sir Ahmadu Bello Memorial Foundation.
Ya ce farfado da masana’antar na daga cikin matakan da gwamnatin Tinubu ke ɗauka domin raya masana’antu da kawo ci gaba a dukkan sassan ƙasar.
Taron wanda ya samu halartar ministoci, shugabannin hukumomin gwamnati da wasu manyan jami’an tsaro daga Arewa Daily Nigerian ta ruwaito cewa ya dauki hankalin jama’a.



