Gwamnatin Tarayya na iya sake sayar da kamfanonin raba wutar lantarki guda 11 (Discos) idan kudirin gyaran dokar lantarki na 2025 ya zama doka.
Kudirin, wanda Sanata Enyinnaya Abaribe ya dauko, na nufin tilasta wa kamfanonin su saka sabon jari cikin shekara guda ko kuma su fuskanci hukunci irin su karancin hannun jari, kwace ko sake cefanarwa.
Jaridar Punch ta tattaro cewa majalisa ta ce matakin zai koma bayan da aka samu tun bayan dokar 2023. Sai dai kungiyar kwamishinonin makamashi ta soki kudirin, tana cewa hakan na iya rusa cigaban da aka samu a sabon tsarin kasuwancin wutar lantarki.
Yanzu haka dai kamfanonin Discos 11 da abin zai shafa sun hada da na Abuja, Benin, Eko, Enugu, Ibadan, Ikeja, Jos, Kaduna, Kano, Port Harcourt da Yola.



