Ministoci da manyan jami’an gwamnatin Shugaba Bola Tinubu sun hallara a Arewa House, Kaduna, domin bayyana nasarorin da gwamnatin tarayya ta cimma cikin shekaru biyu da suka gabata.
Taron wanda gidauniyar Sir Ahmadu Bello Memorial Foundation (SAMBF) ta shirya, ya baiwa shugabannin siyasa, na gargajiya da na addini daga jihohin Arewa 19 damar tattaunawa da wakilan gwamnati a ranar Talata da Laraba.
Rahoton jaridar Premium Times ya ce taron na nazartar yadda gwamnatin Tinubu ta aiwatar da alkawuran da ta dauka a lokacin kamfen din 2023, musamman wadanda suka shafi yankin Arewa.
A shekarar 2021, Shugaba Tinubu ya yi kira da a zuba jari sosai wajen samar da ayyukan yi domin shawo kan matsalolin tsaro da tattalin arziki a yankin.



