Sakataren Gwamnatin Tarayyar Nijeriya, Sanata George Akume, ya shawarci ‘yan siyasa daga yankin Arewa da su dakata har zuwa shekarar 2031 kafin su nemi kujerar shugaban kasa.
Akume ya bayyana haka ne a ranar Talata yayin wani taron tattaunawa na kwanaki biyu a Kaduna, wanda aka shirya domin karfafa hulɗa tsakanin gwamnati da ‘yan ƙasa.
Jaridar Punch ta ruwaito Akume na yabawa cibiyar Sir Ahmadu Bello bisa samar da dandalin tattaunawa domin inganta shugabanci da dimokuraɗiyya a ƙasar.

Ku jira sai zuwa 2031 tukuna – Shawarar George Akume kenan ga ‘yan siyasar Arewa da ke neman kujerar shugaban kasa
-