Uwargidar shugaban Nijeriya, Remi Tinubu, ta sanar da bayar da tallafin naira biliyan ɗaya ga iyalan da rikicin makiyaya ya raba da muhallansu a Jihar Benue.
Ta bayyana hakan ne a ziyarar jaje da ta kai a Benue, inda ta ce tallafin daga shirin Renewed Hope Initiative (RHI) ne domin taimaka wa waɗanda suka rasa matsugunnai su koma gidajensu.
Harin wanda ya faru a Yelewata a watan Yuni, ya yi sanadin rayukan mutane sama da 100 tare da raba wasu da dama da muhallansu.



