Mai bai wa shugaban Nijeriya shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, ya ce hare-haren Boko Haram, ‘yan bindiga da rikicin kabilanci sun ragu matuka a yankin Arewa cikin shekaru biyu da suka gabata karkashin mulkin Bola Tinubu.
Ribadu ya bayyana cewa a lokacin mulkin baya, mutane 1,192 ne aka kashe a Kaduna, yayin da aka sace fiye da 3,348.
Rahoton gidan talabijin na Channels ya ambato Nuhu Ribadu na cewa, fiye da mutane 5,000 ne suka rasa rayukansu a Jihar Benue a cikin wannan lokaci.
Saidai gwamnatin na aiki iyakar karfinta wajen tabbatar da zaman lafiya tsakanin al’umma da kabilun Nijeriya.



