Shugaban kungiyar gwamnonin Arewa kuma gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya cika alkawuran da ya dauka a zaben 2023, yana mai cewa “har yanzu yana ci gaba da cikawa.”
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito Inuwa Yahaya ya bayyana hakan ne yayin wani taron kwanaki biyu da Gidauniyar tunawa da Sir Ahmadu Bello (SAMBF) ta shirya a Arewa House, Kaduna, domin karfafa hulda tsakanin gwamnati da ‘yan kasa.
Inuwa Yahaya ya ce taken taron shine “Binciken Alkawuran Zabe: Karfafa Hulda Tsakanin Gwamnati da Jama’a Domin Hadin Kan Kasa” na nuni da ginshikin dimokuradiyya, inda ya jaddada cewa mulki nagari yana bukatar ci gaba da tattaunawa tsakanin shugabanni da al’umma.



