Asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF ya sanar da Ms. Wafaa Saeed Abdelatef a matsayin wakiliyar asusuna Najeriya.
Kafin ta hau wannan mukami a Nijeriya, Ms Wafaa, ita ce wakiliyar asusun UNICEF a kasar Somalia.
Wafaa na da fiye da shekaru 20 tana yin hidima ga jama’a ta hanyar ayyukan Majalisar Dinkin Duniya. Ta yi aiki da OCHA, UNICEF da WFP a wurare masu fama da rikice-rikice da matsaloli masu tarin yawa, inda ta samu kwarewa wajen gudanar da shirye-shirye da hada kai tsakanin ayyukan jin kai da ci gaba. Ta yi ayyuka a kasashen sun hada da Sudan, Somalia, Indonesia, Pakistan, Syria da Ethiopia. Ta kuma rike manyan mukamai na shugabanci a OCHA, duka a New York da Geneva.
Kafin ta shiga tsarin Majalisar Dinkin Duniya a shekarar 2000, Wafaa ta yi aiki da kamfanoni masu zaman kansu, jami’o’i da kungiyoyin farar hula a kasar Sudan, inda ta mayar da hankali kan shirye-shiryen taimaka wa ‘yan gudun hijira da kuma kare muhalli.
Wafaa ta samu digiri na biyu (Master’s) a fannin zane-zanen gine-gine daga Jami’ar Katholieke Universiteit Leuven da ke kasar Belgium, digiri na biyu a fannin Tsarin Birane daga Jami’ar Khartoum, da kuma digiri na farko (Bachelor) a fannin zane-zanen gine-gine daga Jami’ar Khartoum, Sudan.