Kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) ta bayyana damuwarta kan yadda yankin Arewa ke fuskantar wariya wajen rabon kasafin kuɗi da aiwatar da manyan ayyuka a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Shugaban kwamitin amintattu na ACF, Alhaji Bashir M. Dalhatu, ne ya bayyana haka a taron tattaunawa da Sir Ahmadu Bello Memorial Foundation ta shirya a Kaduna.
Dalhatu ya ce abin takaici ne ganin yadda ake yi wa yankin Arewa watsi da muhimman ayyukan ci gaba duk da irin gudunmuwar da yankin ya bayar wajen nasarar Tinubu a zaben 2023.
Ya jaddada cewa wannan lamari rashin adalci ne ga yankin da ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa wannan gwamnati.