Wani saurayi a unguwar Ibadan dake Ebute Meta, jihar Legas, ya lakadawa budurwarsa Fatima, wadda ke sana’ar gyaran kai, dukan da ya janyo ta rasa hakora shida.
Lamarin ya faru ne ranar Asabar, 12 ga Yuli, 2025, bayan wata gajeriyar cacar baki tsakanin masoyan da ta rikide zuwa tashin hankali.
Rahotanni sun nuna cewa Fatima ta kwanta a asibiti sakamakon munin dukan da saurayin nata ya yi mata, lamarin da ya jawo fargaba da kuka daga iyalanta, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.



