DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Dino Melaye ya fice daga jam’iyyar PDP bisa zarginta da gazawa

-

Tsohon Sanatan da ya wakilci yankin Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya sanar da murabus dinsa daga jam’iyyar PDP mai adawa a Nijeriya, yana mai zargin jam’iyyar da rashin iya jagoranci nagari da gaza kawo sauyi ga rayuwar ‘yan Nijeriya.

A cikin wasikar murabus da ya wallafa a shafinsa na X ranar Alhamis, mai dauke da kwanan wata 4 ga Yuli, 2025, kuma aka aika zuwa ga shugaban PDP na mazabar Ward 1, Aiyetoro Gbede, karamar hukumar Ijumu a jihar Kogi, Melaye ya bayyana cewa ya fice gaba daya daga dukkan harkokin jam’iyyar nan take.

Google search engine

Melaye, wanda ya tsaya takarar gwamnan Jihar Kogi a ƙarƙashin jam’iyyar PDP a zaben 2023, ya bayyana cewa matakin da ya ɗauka ya biyo bayan zurfin tunani ne game da halin da jam’iyyar ke ciki da kuma inda take nufa a gaba.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttp://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Babban Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Za mu fara hukunta duk wani dan kasar waje da wa’adin bizarsa ya kare a Nijeriya kuma ya ci gaba da zama – Gwamnatin...

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa yanzu tana da cikakken tsarin gano tare da cafke baƙin ƙasashen waje da suka wuce wa’adin zaman da aka ba...

Obasanjo ya nuna jarumtaka da sadaukarwa wajen yi wa Nijeriya hidima – Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo murnar cika shekaru 89 da haihuwa. A cikin wata sanarwa da mai magana da...

Mafi Shahara